in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomi sun amsa tambayoyi kan aikin kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje
2016-11-10 10:44:01 cri
Hukumomin kasar Sin na aiwatar da doka sun amsa a ranar Talata ga tambayoyi kan makomar aikin kungiyoyi masu zaman kansu (ONG) na yammacin duniya dake kasar Sin, a kusantowar fara aikin wata sabuwar doka kan ONG din kasashen waje da aka tsai da a cikin watan Janairun shekarar 2017.

A yayin wani takaitaccen bayani a ranar Talata a birnin Shangahai da ma'aikatar tsaron jama'a da cibiyar tsaron jama'a ta Shanghai suka gabatar, ma'ailatar ta tabbatar da cewa ba za a samu wani lokacin wucin gadi ba domin ONG din kasashen waje.

Kungiyoyi masu zaman kansu na yammacin duniya ya kamata su shirya bisa ga sabon mataki kana hukumomi suna neman wasu sabbin hanyoyin domin tallafa musu, in ji ma'aikatar.

Cibiyoyin wakilcin kungiyoyin ONG na yammacin duniya na iya shirya ayyukansu a cikin yankunan da aka yi rijista.

Da ake tabo ayoyi na 10 dana 13 na doka, ma'aikatar ta jaddada cewa kungiyoyin ONG na yammacin duniya na iya kafa daya ko cibiyoyi da dama na wakilcinsu a kasar Sin kana kuma dole su gabatar da kuma yin rejista a yankunan da zasu yi aiki.

Wannan mataki zai taimaka wajen tantance hukumomi masu aiki wajen kula da ayyukan kungiyoyin ONG na yammacin duniya a fannoni daban daban, kamar tattalin arziki, ilimi da ba da ceto bayan bala'u. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China