Wani bincike da majalissar zartaswar kasar Sin da hadin gwiwar hukumar kididdigar kasar suka gudanar, ya nuna cewa, harkar raya sana'o'i a kasar Sin na samun ci gaba yadda ya kamata, matakin da ke dada karfafa gwiwar masu sana'o'i daban daban.
Sakamakon wannan bincike wanda aka gudanar kan kamfanoni 1,960 dake sassan kasar ya nuna cewa, alkaluman hasashen matsakaicin karuwar GDPn kasar na shekarar 2016 ya kai kaso 6.5 cikin dari, yayin da na shekarar 2017 mai zuwa ya kai kaso 6.3 cikin dari.
Har wa yau binciken ya nuna yadda masu sana'o'i daban daban ke samun karin kwarin gwiwa game da yanayin tattalin arzikin kasar ta Sin a cikin gida. Sassan da hakan ya shafa kuwa sun hada da na noma da samar da makamashi, da na fasahar sadarwa, da na ba da hayar kayayyaki. Sauran sun kunshi fannin ba da hidima, da na sarrafa magunguna, da kuma na kirar kayayyakin laturoni.(Saminu)