in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a dakatar da buda wuta yayin da al'amura ke kara dagulewa a Syria
2016-09-26 20:28:15 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ja hankalin daukacin sassan kasar Syria da su kai zuciya nesa, su dakatar da bude wuta domin kare rayuwan al'ummar kasar, a daidai wannan lokaci da al'amura ke kara dagulewa a kasar.

Mr. Geng Shuang wanda ya yi tsokacin yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Litinin, ya ce dakatar da bude wuta da kawo karshen kaddamar da hare hare, na cikin muhimman ginshikai na wanzar da zaman lafiya a kasar, matakin da kuma zai bunkasa yanayin jin kai da ake ciki, ya kuma kawo karshen ayyukan 'yan ta'adda a kasar.

A jiya Lahadi ne dai kwamitin tsaron MDD ya kira wani taron gaggawa domin tattauna halin da ake ciki a kasar ta Syria. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China