Hukumar shirya wasanni ta shiyyar kudancin Amurka wato (Conmebol) ce ta sanar da kulub din a matsayin wanda ya lashe gasar kofin kwararru ta shekarar 2016, kamar yadda kungiyar wasan da zasu kara wato Atletico Nacional ta bukaci yin hakan.
A makon jiya ne dai tawagar kulub din na Chapecoense ta gamu da harin jirgin sama a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Medellin, na kasar Colombiya, inda aka shirya murza leda tsakaninsu da Atletico a yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da wasannin karshe.
Kamfanin dillancin labarai na EBC na kasar Brazil ya ambato cewa, daga cikin lambar yabon, kulub na Brazil zai karbi tsabar kudi har dalar Amurka miliyan biyu, da kuma samu damar shiga wasannin Copa Libertadores de America a shekarar 2017.
Atletico Nacional kuma zai karbi lambar yabo ta Conmebol, wanda ya kunshi kudi dalar Amurka miliyan guda.
Domin samun bunkasuwar zaman lafiya ne yasa ake shirya wasannin kwallon kafa na kudancin shiyyar Amurka, kamar yadda aka bayar cikin wata sanarwa a helkwatar hukumar dake Asuncion, na kasar Paraguay cewar, don tabbatar da samun fahimtar juna da adalci, bisa la'akari da kasancewar matsayin wasannin motsa jiki ya zarta samun kudade kawai, shi yasa majalisar ta yanke shawarar cewa zata baiwa kulub din Atletico Nacional matsayi na biyu a wasannin.(Ahmad Fagam)