Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya tattauna a ranar Litinin a birnin Lome tare da Dora Siliya, ministar noman kasar Zambiya, kan matakan da za su dauka domin ganin cewa, takarar Togo kan kujerar komishinan harkokin tattalin arziki na kwamitin tarayyar Afrika (AU), da kuma takarar Zambiya kan kujerar kwamishinan kasuwanci, masana'antu da noma, sun sami nasara a yayin zabukan watan Janairu mai zuwa.
A cikin watan Janairun shekarar 2017, kungiyar AU za ta zabi wani sabon shugaban kwamitin domin maye gurbin 'yar kasar Afrika ta Kudu, madam Nkosazana Dlamini Zuma. Sabon mutumin da zai tafiyar da aikinsa tare da taimakon wani mataimakin shugaba, da kuma wasu kwamishinoni guda takwas. (Maman Ada)