in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Togo za ta karbi bakuncin bikin raye raye na kasa da kasa
2016-11-21 11:17:26 cri

Bikin kasa da kasa na raye rayen gargajiya da na zamani karo na 5 da aka fi sani da "Baare" zai gudana daga ranar 25 zuwa 27 ga wata a birnin Lome na kasar Togo, in ji shugabar kungiyar SOJAF, madam Sodji Dede Dzigbode, kuma shugabar wannan bikin.

Ta bayyana cewa, bikin wannan karo zai samu halartar 'yan wasan Togo, Benin, Cote d'Ivoire da kuma Ghana.

Burin mu shi ne yin aiki wajen karfafa cudanyar al'ummomi shiyyar, musammun ma sanya matasa cikin aikin kiyaye da zamanintar da kuma watsa al'adun gargajiya na kakanni da kakanni da ba na kayayyaki ba, in ji madam Sodji.

A yayin bikin, za a shirya bukukuwa daban daban da su hada da wani ayarin 'yan wasan, wakoki da raye rayen gargajiya da na zamani, wasannin kide kide da rayawa, faratin kayan duwatsu masu daraja, wasannin kwakwaiyon 'yar tsana, nuna fuskokin butun butumi da kuma baje kolin duwatsu masu daraja, in ji madam Sodji.

Tun a shekarar 2012, kungiyar SOJAF take shirya a ko wace shekara, wani bikin kasa da kasa na raye rayen gargajiya da na zamani tare da gayyato kungiyoyin wasannin fasaha, da raye rayen gargajiya da na zamani na kasashe makwabta domin musanyar kwarewa tare da kungiyoyin 'yan wasan fasaha na kasar Togo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China