in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambiya ta yi bikin cika shekaru 52 da samun 'yancin kai
2016-10-25 10:27:00 cri

A jiya Litinin kasar Zambiya ta yi bikin cika shekaru 52 da samun 'yancin kanta. Taken bikin na bana shi ne "amfani da 'yancin kanmu da hadin kan kasa domin daga martabar Zambiya".

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, wanda shi ne babban bako a bikin ya bayyana cewa, hanya daya tilo da kasashen nahiyar Afrika za su magance kalubalen da suke fama da shi a halin yanzu shi ne, lalibo hanyoyin karfafa hulda a tsakanin kasashen na Afrika.

Ya ce, matsaloli da dama dake addabar Afrika suna faruwa ne sakamakon gazawar 'yan kasar ta gano hakikanan abubuwa, da matsalar tsaro, da talauci, da rashin sanin makoma.

Museveni ya ce, kamata ya yi Afrika ta kara hanyoyin sarrafa kayayyaki a cikin gida domin shawo kan kalubalen dake addabar matasa, musamman matsalar rashin aikin yi, da yunwa, inda ya kara yin kira da a martaba kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa.

A cewarsa, lokaci ya yi da masu zuba jari su ba da muhimmanci ga kayayyakin da masana'antu ke bukata wanda ake samar da su a nahiyar don samar da guraben ayyukan yi ga al'umma.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China