in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Togo ya yi maraba da kokarin da aka yi wajen cimma kundin AU kan tsaron teku
2016-10-17 10:14:02 cri

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika (AU) da suka halarci taron gaggawa kan tsaron teku da ci gaban Afrika a ranar Asabar a Lome sun taimaka wajen cimma da rattaba hannu kan kundin Lome.

Shugaban Togo Faure Gnassingbe ya tabo a karon farko matsalar tattalin arziki ta hanyar ruwan teku a cikin watan Yunin shekarar 2014 a yayin taron kungiyar tarayyar Afrika (AU) a Malbo a kasar Guinea Equatorial.

Tun lokacin shugaba Faure Gnassingbe da kansa ne ya himmatu wajen tafiyar da aikin kundin a Lome har zuwa kammala sa.

Rattaba hannu ga kundin Lome kan tsaron teku da ci gaba a Afrika wani abin farin ciki bayan tsawon lokaci da aka dauki, lamarin da ya soma daga wani tunani na Faure Gnassingbe.

A cewar shugaban Congo, Denis Sassou N'Guesso da ya karanta sanarwar godiya kan wannan nasara, ya nuna wa shugaban Togo babban yabo da karramawa na dukkan nahiyar da ma takwarorinsa.

Ayyukan taron sun taimaka wajen karfafa kungiyar kasashen domin yaki da rashin tsaro kan ruwan tekun Afrika. Haduwar ta musammun ta Lome za ta taimaka kuma ga bangarorin dake kula da ruwan tekun Afrika daban daban da su yi aiki tare. Wannan na hada shata kan iyakokin ruwa da samar da kayayyakin soja yadda ya kamata domin tsaron tekun Guinea, in ji shugaban na Congo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China