Ana gudanar da binciken ne bisa hadin gwiwa da kamfanin Arik Air, da hukumomin kasar Afirka ta Kudu, in ji Sam Adurogboye, kakakin hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta NCAA, wanda ya fadi haka a birnin Ikko. Ya kuma kara da cewa, bayan da aka kammla binciken, gwamnatin kasar za ta dauki matakin da ya wajaba, sai dai har yanzu ba a san wane ne wannan mutum da ya rasa ransa.
A nasa bangaren, kamfanin Arik Air shi ma ya ce, ba shi da wani bayani dangane da batun, sai bayan da aka kammala binciken lamarin.
An gano gawar mutumin ne a ranar Laraba, a cikin rijiyar wili na wani jirgin saman kamfanin Arik mai samfurin A330-200, bayan da jirgin ya sauka a filin saukar jiragen sama na Oliver Tambo da ke birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu.(Bello Wang)