in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin majalisun Sin da Aljeriya sun yi ganawa
2016-12-03 13:29:42 cri
A jiya Jumma'a, Mista Zhang Dejiang, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya gana da takwaransa na majalisar dokokin kasar Aljeriya Mohamed Larbi Ould Khelifa, a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A cewar shugaban majalisar dokokin kasar ta Sin, shugabannin kasashen 2 sun yanke shawara a shekarar 2014, don kafa hulda game da manyan tsare-tsare tsakanin kasashen 2, hakan na alamantar ci gaban huldarsu zuwa wani sabon mataki. Jami'in ya ce, kasar Sin za ta tsaya kan manufofinta na hulda da kasashen Afirka, don karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Aljeriya.

Mista Zhang, ya kara da cewa, majalisar dokoki tana taka muhimmiyar rawa ta fuskar siyasa ga kowace irin kasa, kuma za ta iya samar da gudummawa ta musamman wajen karfafa huldar dake tsakanin bangarorin 2. Saboda haka yana fatan ganin majalisun kasashen 2 za su kara yin hadin kai, don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin bangarorin 2.

A nasa bangaren, shugaban majalisar dokokin kasar Aljeriya, ya nuna yabo game da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma, tare da fatan ganin karin hadin gwiwar da bangarorin Aljeriya da Sin za su yi kan ayyuka daban daban.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China