in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar sana'ar tsimin makamashi a kasar Sin ta wuce kashi 2% na GDP
2016-11-29 11:56:48 cri
Zuwa karshen shekarar 2015, karuwar kudin kayayyakin da ake samarwa a fannin aikin tsimin makamashi da kiyaye muhalli na kasar Sin ta kai kimanin kashi 2.1% na adadin kayayyakin da ake samarwa a gida wato GDP na kasar Sin. Haka zalika an kiyasta cewa, zuwa shekarar 2020, karuwar da za a samu a wannan fanni za ta wuce kashi 3% na GDP din kasar.

Hu Zucai, mataimakin darektan kwamitin kula da ci gaba da gyare-gyare na kasar Sin, ya sanar da hakan a jiya Litinin, yayin taron baje kolin kayayyakin tsimin makamashi na kasa da kasa, wanda ke gudana a garin Zhenjiang na lardin Jiangsu dake gabashin kasar ta Sin.

A cewar jami'in, tun daga zuwa karshen shekarar 2015, yawan kudin kayayyaki dake da alaka da aikin tsimin makamashi da aka samar da su ya kai kudin Sin Yuan biliyan 4500, kana sana'ar samar da kayayyakin ta shafi ma'aikata miliyan 30. Haka zalika, yanzu a wannan bangare, ana samun wasu manyan kamfanoni fiye da 70, wadanda kudin shigar kowanensu a duk shekara ya zarce Yuan biliyan 1. Ban da haka kuma, ana kyautata zaton cewa, zuwa shekarar 2020, yawan kudin kayayyakin da kamfanonin bangaren tsimin makamashi da kiyaye muhalli na kasar Sin suke samar zai kai fiye da Yuan biliyan dubu goma.

Ban da wannan kuma, a nashi bangare, mista Yang Weimin, mataimakin darektan ofishin kula da aikin kudi na kasar Sin, ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta cimma burin da ta saka a gabanta wajen kiyaye muhallin halittu. Sa'an nan bisa wani sabon shirin raya kasa da ta tsara, ta riga ta samu damar rage amfani da makamashi da kashi 5.2%, da rage konar kwal da kashi 2%, a farkon watanni 9 na shekarar 2016. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China