in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na Saliyo
2016-12-01 20:52:02 cri

A yau Laraba ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na Saliyo, Ernest Bai Koroma a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, inda suka kuduri aniyyar daga matsayin dangantaka tsakanin kasashen biyu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a duk fannoni, da zurfafa hadin gwiwa a duk fannoni domin sada zumunci da samun moriyar juna, da nufin tabbatar da sakamakon da aka samu a taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, a kokarin kara kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare, shugaba Koroma ya bayyana cewa, Sin aminiyar Saliyo ce ta hakika. A shekarar 2014, yayin da kasar Saliyo take fama da cutar Ebola, Sin ta ba ta taimako nan take, tare da yin kira ga sauran kasashen duniya da su taimaka mata. Ya sake nuna godiyarsa ga shugaba Xi, da gwamnatin kasar Sin, da kuma jama'ar kasar, shugaba Koroma ya ce,wannan ya burge jama'ar Saliyo kwarai da gaske.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China