in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan Kungfu na Taichi
2016-11-09 16:12:05 cri


Masu sauraronmu sun rubuto mana cewa suna sha'awar wasan Kungfu na kasar Sin sosai, don haka suna son sauraron bayani dagane da ire-iren wasannin Kungfu na kasar Sin. Don biyan bukatunsu, a cikin shirinmu na yau, za mu yi magana kan wani shahararren wasan kungfu na kasar Sin mai tarihi sosai, wanda ke samun karbuwa matuka a sassan daban daban na kasar Sin, har ma a duk duniya. Sunan wasan shi ne Taichi.

Ma'anar kalmar 'Taichi'

Da farko za mu yi bayani kan ma'anar kalmar ' Taichi'. Taichi dai wani zane ne na musamman, wanda masu ilimi na da na kasar Sin sukan yi amfani da shi don nuna yanayin da abubuwan duniya suke ciki. Zanen mai siffar da'ira, an raba shi zuwa bangarori 2, daya fari ne, dayan ma baki, sa'an nan cikin bangaren fari akwai wata karamar da'ira mai launin baki, yayin da cikin bangaren baki ma akwai wata da'irar mai launin fari.

Ta wannan zane, ana iya bayyana rabe-raben abubuwa ko halittun duniya zuwa gida 2 masu sabawa juna. Ga misali, fari da baka, zafi da sanyi, namiji da mace, da dai sauransu. Sa'an nan, idan an nazarci zanen, za a ga dukkan bangarorin 2 suna cikin wani tsari mai juyawa, kuma hakan na nufin idan wani abu ya kai wani matsayi mai tsanani, to, ya kan juya zuwa wani bangare sabanin haka.

Kamar idan yanayi ya zama mai zafi, to zai fara zama mai sanyi sannu a hankali. To, kamar a da muka bayyana dangane da zanen Taichi, za a fahimta cewa kalmar Taichi tana da ma'ana mai zurfi, wadda ta bayyana ra'ayin Sinawa dangane da daukacin abubuwa ko halittu na duniya. Sai dai a nan an yi amfani da wannan babbar kalma wajen kiran wasan. Wannan ya nuna mana cewa, wasan Taichi wata fasaha ce mai zurfi, wadda ta kunshi amfani a bangarori daban daban.

Wasan Taichi, idan an yi shi sannu a hankali, zai zama wata dabara mai kyau wajen motsa jiki da kiwon lafiya. Amma idan an hada fasaharsa cikin wasan dambe, to, za a iya samun wata irin fasahar dambe mai karfi. Ta haka kuma yana iya zama kai kayatarwa ga mutane, kuma za a iya gudanar da gasa tsakanin 'yan wasan sa, kamar yadda ake gudanar da gasannin wasan dambe na zamani.

Asalin wasan Taichi

A karni na 17, wani mutum mai suna Chen Wangting, ya gaji fasahar Kungfu daga iyalinsa, sa'an nan ya kama aikin mai tsaron ayari. Wato yana amfani da fasaharsa ta wasan Kunfu wajen kare ayarin masu jigilar kaya daga hare-haren 'yan fashi. Saboda kwarewarsa a fannin wasan Kungfu, ko ina ya nufa 'yan fashi kan ji tsoro sun gudu.

Bayan da wannan mutum ya tsufa, ya yi ritaya a gida. Daga bisani ya fara hada fasaharsa ta Kungfu da fasahohin wasannin dambe na wurare daban daban, ta yadda ya kirkiro wani sabon nau'in wasan Kungfu na musamman, wanda ya sawa suna Taichi.

Bayan da Chen ya kirkiro fasahar wasan Taichi, ya kuma yi fatan iyalinsa su koyi wannan fasaha, amma bai yi niyyar yada ta zuwa ga sauran mutane ba. Amma sannu a hankali fasahar ta zama sananniya a wurare daban daban, inda mutane da yawa suke sha'awar koyon ta. Don haka, daga bisani, fasahar wasan Taichi ta yadu zuwa wurare daban daban na kasar Sin, har ma ta rabu zuwa nau'oi daban daban.

Ire-iren fasahohin wasan Taichi

Bayan da Chen Wangting ya kirkiro wasan Taichi wasu shekaru fiye da 300 da suka wuce, mutane suna ta kokarin nazarin fasahar wasan, da yada ta zuwa wurare daban daban. Irin gyaran da ake yi kan fasahar yayin yaduwarta, ta sa ake samun nau'o'i daban daban na fasahar a yanzu.

Ga misali, akwai Taichi irin ta Chen, wato na asali da Chen Wangting ya kirkiro. Ban da shi kuma, akwai irin Taichi na Yang, da na Wu, da na Sun, da dai sauransu. A gundumar Wen, inda iyalin Chen Wangting suka rayu, ana koyar da Taichi irin na Chen. Yayin da a gudumar Yongnian, ake koyar da irin na Yang da na Wu. Sa'an nan a nan birnin Beijing, Taichi da ya fi yaduwa su ne nau'in na Wu, da na Sun.

Duk wadannan nau'o'in Taichi, tsare-tsaren motsinsu kusan iri daya ne. Sai dai za a iya bambanta su bisa wasu motsi na musamman da kowannen su ke da shi. Wasun su na da tsarin da ya fi sarkakiya, da kuma motsi mai wuya, wadanda suka dace da koyo ga matasa. Yayin da wasu daga cikinsu tsarinsu ya fi sauki, don haka ya dace da tsofafi su koya.

Yanayin musamman na wasan Taichi

Wasan Taichi yana da wani yanayi na musamman, wanda ya sha bamban da na sauran fasahohin wasan dambe. Yana bukatar a tsaya don jiran a matso kusa, sa'an nan a karkata bugun da aka yi, a juya shi zuwa wani gefe, daga baya a kai hari ga wurin da ba shi da kariya sosai.

Irin motsin da ake yi cikin wasan Taichi, ya hada da juya hannun mutum, da bugu da gwiwar hannu, da buga da kafada, da dai sauransu. Motsin da ake amfani da su yayin da mutane 2 suke tsaye kusa da juna sosai.

Tarihin raya wasan Taichi bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a 1949

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, wasu shugabannin kasar da suka hada da Mao Zedong, da Deng Xiaoping, sun taba kira ga jama'ar kasar da su kara shiga wasan Tachi, don samun lafiyar jiki.

Sa'an nan bayan da kasar ta fara daukar manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, an samu damar bude kasuwannin kasar. Irin ci gaban da aka samu a fannin tattalin arziki, ya sa aka fara kokarin habaka aikin koyar da fasahar Taichi ga jama'a.

Don samun saukin koyon fasahar Taichi, hukuma mai kula da harkar wasanni ta kasar Sin ta sanya aka saukaka fasahar wasan Tachi zuwa motsi 24, sa'an nan aka yi kokarin yada fasahar tsakanin al'ummar kasar Sin. A birnin Beijing kawai, an samu wuraren koyar da wasan Taichi fiye da 140 a shekarar 1980, inda aka samu damar horar da mutane fiye da dubu 40.

Yanzu haka a gundumar Wen, inda iyalin Chen Wangting wanda ya kirkiro fasahar wasan Taichi suka rayu, akwai makarantun koyar da fasahar Taichi fiye da 30, inda dalibai masu koyon fasahar yawansu ya kai kimanin 8000. Ban da haka kuma wasu mutane fiye da 300 da suka koyi fasahar Taichi a makarantun gundumar Wen, suma tuni sun samu kwarewa sosai a wannan fanni, sun kuma bude makarantu na koyar da wasan Taichi fiye da 300 a wurare daban daban.

Baya ga yaduwar fasahar Taichi a cikin kasar Sin, an kuma yada fasahar zuwa kasashe da yankuna daban daban fiye da 150, ta yadda aka sanya wasan Taichi ya zama daya daga cikin wasannin dambe mafiya yaduwa da farin jini a duniya. An kiyasta cewa, yawan mutanen da suke koyon fasahar wasan Taichi ya kai kimanin miliyan 300, a daukacin duniya.

Amfanin koyon fasahar wasan Taichi

Duk da cewa lokacin da aka kirkiro wasan Taichi, an yi shi ne domin koyon fada. Amma a yanzu, mafi yawan mutane suke koyon fasahar wasan Taichi na koya ne saboda motsa jiki da kiwon lafiya.

Idan aka dubi wasan Taichi, za a gane cewa wasa ne da bai kebanta kan motsa sassan jiki kawai ba, domin kuwa ya shafi yadda ake tunani da kuma numfashi. Don haka, lokacin da ake wasan Tachi, ban da motsa jiki, ana kuma samun damar daidaita numfashi da motsi, ta yadda zai amfani kayan cikin mutum.

Kafin a fara wasan Taichi, za a bukaci samun kwanciyar hankali, sa'an nan a mai da dukkan tunani kan wasan kadai. Ta wannan hanya za a iya sanya hankalin mutum ya nutsu sosai.

Ban da haka kuma, a kan kwashe rabin sa'a ko sa'a daya, wajen kammala wasan Taichi a ko wane karo, wanda hakan ke sanya mai yin wasan motsa jikinsa sosai, da karfafa gudanar jininsa. Hakan yana da amfani ga lafiyar jikinsa sosai.

Haka zalika, fasahar numfashi na musamman da ake amfani da ita yayin da ake wasan Taichi, tana da amfani ga kyautatar lafiyar huhu, da zuciyar mutum. Kuma za ta taimaka wajen rage damar kamuwa da cututtukan da suka hada da hawan jini, da ciwon zuciya, da dai makamantansu.

Abin da ya kamata a lura da shi yayin da ake wasan Taichi, shi ne duk wani amfani da ke tattare da wasan, ba a iya ganinsa cikin wani dan gajeren lokaci. Ana bukatar a dinga yin wasan Taichi a kai a kai, ta yadda sannu a hankali amfanin wasan zai fara bayyana. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China