in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Salon wasan Kungfu na zamani
2016-10-19 15:46:14 cri

Idan mun dubi kalmar Kungfu, ya kamata mu bayyana cewa kalma ce da mutane da dama a duniya suke amfani da ita don bayyana fasahar motsa jiki da fadace-fadace ta gargajiyar kasar Sin, wadda aka fara saninta bisa kallon wasu tsoffin fina-finan da aka dauka a yankin Hongkong na kasar Sin, wadanda suka sanya 'yan wasan kwaikwayo irinsu Bruce Lee da Jackie Chen suka zama sannannu a duk duniya.

Sai dai a nan kasar Sin, an fi amfani da kalmar 'Wu Shu' a matsayin sunan irin wannan fasahar gargajiya ta motsa jiki da fadace-fadace. Idan an yi nazari kan kalmar sosai, za a gano cewa, 'Shu' na nufin fasahohi, yayin da 'WU' ke nufin fadace-fadace, da kuma wata ma'ana mai zurfi ta 'hana daukar makamai'.

Don haka sunan fasahar na nuna mana cewa, ana wannan wasa ne ba domin fada ba, maimakon haka ana yin sa ne domin kare kai, da kuma magance fadace-fadace tsakanin mutane.

Yanzu haka a nan kasar Sin za a iya raba fasahohin Wu Shu zuwa gidaje 3. Wato na farko, irin wasannin da ake nuna su a matsayin wata fasahar motsa jiki mai ban sha'awa. Za a iya nuna su ga mutane, ko kuma shirya gasa ta musamman cikin su, inda 'yan wasa suke gwada fasaharsu, ta yadda za a iya gane wane ne daga cikinsu ya fi saura ta fuskar kwarewa a fannin motsa jikin sa, kuma ko yanayin wannan motsi yana da wuya ko akasin hakan.

Salo na biyu na wasan Wu Shu na kasar Sin a halin yanzu shi ne, irin wasan da ake tsarawa, domin ya dace da ka'idojin wasannin zamani, wato domin a gudanar da gasa a cikin wani dandali, kwatankwacin yadda ake gudanar da wasan dambe ko kuma 'boxing' a Turance. Sai dai wannan wasan da ake yi a nan kasar Sin, ya yarda a yi amfani da hannu, da kafa, da fasahar kokawa, yayin da 'yan wasa suke takara da juna. Hakan ya nuna cewa wasan Wu Shu na kasar Sin bai tsaya kan fasahar hannu ko ta kafa kadai ba. Ya shafi dukkan sassan jikin mutum, gami da fasahohin fadace-fadace irin daban daban.

Sa'an nan salo na uku na wasan Wu Shu na kasar Sin, shi ne ire-iren wasannin fadace-fadace na gargajiya da suke yaduwa tsakanin al'ummomin kasar. Wadannan fasahohin an gaje su daga kaka da kakanni, haka kuma jama'a suna kokarin yada su ga zuriyoyi masu zuwa. Cikinsu akwai wasan Taichi ko kuma 'Shadow Boxing' a Turance, da wasannin Wu Shu irin na haikalin Shaolin, da wasan WingTsun dake samun karbuwa a kudancin kasar Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China