Julian Weigl dan shekaru 21 da haihuwa, wanda wannan ce kakar wasa ta biyu da yake bugawa Dortmund din wasa, ya nuna kwarewa matuka a fagen taka leda, kuma tuni kocin Dortmund din Thomas Tuchel ya jinjinawa kwazon wannan dan wasa.
Wasu manazarta harkokin wasanni dai na ganin cewa, kungiyar dake sahun gaba wajen hamayya da Borussia Dortmund wato Bayern Munich, za ta yi da-na-sanin rashin daukar wannan matashin dan wasa tun da wuri, duba da cewa Weigl din ya fara wasa ne kusa da kungiyar ta Munich. Domin kuwa an haifi Weigl ne a wani gari dake kusa da birnin na Munich, ya kuma yi wasa a kungiyar 1860 Munich, kungiyar kwallon kafa ta biyu mafi karfi a birnin, kafin Borussia Dortmund ta saye shi kan kudi euro miliyan 2.5.
Rahotanni sun nuna cewa kungiyar 1860 Munich ta sayi Weigl ne bayan da ta gano kwarewar sa a wata gasar kwallon kafa da aka bugawa tsakanin 'yan wasa biyar-biyar.
A yanzu haka kuwa Weigl ya fara nunawa duniya basirar sa a fagen tamaula, ta yadda wasu alkaluman kididdigar kwarewar 'yan wasa suka nuna cewa, mai yiwuwa ne matashin dan wasan ya shiga jerin kwararrun 'yan kwallon tsakiya kamar su Toni Kroos, da Luka Modric da kuma Sergio Busquets.
A wannan kaka ta wasanni, Weigl ya samu kaso 92.9 bisa dari a yawan mika kwallo, sama da kaso da 'yan wasa irin su Modric da Busquets suka taba samu. Kaza lika a gasar Bundesliga ta farko da ya buga, dan wasan ya samu kaso 91.8 na mika kwallo cikin nasara. Har wa yau yayin wasan Real Madrid da Durtmund wanda suka tashi 2 da 2, Weigl ne ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar kungiyar sa. Matakin da ya sanya ake rade-radin cewa mai yiwuwa nan gaba kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi zawarcin Weigl.(Saminu Alhassan)