in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da nuna damuwa game da tashe-tashen hankula a yankin Darfur
2016-03-04 09:48:12 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, da shugabar kwamitin zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Nkosazana Dlamini-Zuma, sun bayyana rashin jin dadin su, game da tashe-tashen hankula da ke ci gaba da wakana a yankin Darfur na kasar Sudan.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan, a yayin ganawar sa da 'yan jaridu a jiya alhamis, yana mai cewa jami'an biyu sun nuna matukar damuwa game da halin matsi da fafaren hula ke fuskanta, a sakamakon fadan da ake gwabzawa a yankin Jebel Marra, tsakanin dakarun gwamanati da na 'yan tawayen SLA reshen Abdul Wahid.

Sakamakon hakan ne kuma jami'an biyu, suka yi kira ga gwamnatin kasar Sudan, da ta yi hadin gwiwa da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake yankin wato UNAMID, wajen samar da damar zirga-zirga, tare da shigar da kayan tallafin jin kai ga mazauna yankin.

An dai kwashe kusan makwanni 6 ana musayar wuta a wannan yanki na Darfur, lamarin da ya raba fararen hula sama da 90,000 daga matsugunnan su a arewacin Darfur, baya ga wasu mutanen miliyan 2 da dubu dari 6 wadanda tuni yakin ya kora daga yankin.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China