in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata tawagar AU ta kammala ziyararta a Sudan ta Kudu tare da niyyar ci gaba da kokari domin zaman lafiya
2016-11-02 10:51:41 cri

Kungiyar tarayyar Afrika wato AU ta yi alkawarin ci gaba da tattaunawa tare da bangarori masu gaba da juna a Sudan ta Kudu domin maido da zaman lafiya da zaman karko a cikin wannan kasa da yaki ya lalata.

Wadannan kalamai an yi su ne a ranar Litinin da yamma a albarkacin kammala ziyarar aiki ta kwanaki uku a Juba ta wata tawagar kwamitin zaman lafiya da tsaro ta kungiyar AU da kwamitin AU.

Shugabar wannan tawaga, Catherine Muigai Mwangi ta bayyana cewa, tawagar ta gana da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir, da mambobin gwamnatin, da kuma wakilan kungiyoyin jin kai dake kasar.

Rikici ya sake barkewa a farkon watan Yuli tsakanin masu biyayya ga shugaba Kiir da kuma dakarun dake goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa na farko, da aka kora, Riek Machar tun lokacin da ya bar Sudan ta Kudu, wanda kuma a yanzu haka yake gudun hijira a Afrika ta Kudu, inda daga can yake yin kira ga magoya bayansa da su kifar da gwamnatin Kiir.

Sabbin tashe-tashen hankali sun janyo daruruwan mace-mace da tilasta wa miliyoyin mutane barin muhallinsu.

Madam Mwangi ta yi kira ga 'yan Sudan ta Kudu da su dakatar da tashe-tashe hankali domin su rungumi hanyar zaman lafiya da tattaunawa.

"Maganarmu ta karshe ita ce ta yin kira ga dukkan 'yan Sudan ta Kudu da su amince da zaman lafiya, da su amince da yin shawarwari", in ji jami'ar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China