Kwamitin sulhun MDD ya gudanar da wani taro a wannan rana, inda aka tattauna kan batun kasar Sudan ta Kudu. A gun taron, Wu Haitao ya bayyana cewa, Sin na goyon bayan jama'ar Afirka game da warware matsalolin nahiyar, da nuna goyon baya ga kungiyar shugabannin gabashin Afirka a kokarin ta na taka muhimmiyar rawa kan warware matsalar kasar Sudan ta Kudu. (Zainab)