Mataimakin mai magana da yawun SPLM-IO, Major Dickson Gatluak, ya ce James Gatdek Dak, shi ne mai magana da yawun Machar, ana tsare da shi a halin yanzu, kuma akwai yiwuwar za'a tisa keyarsa zuwa Sudan ta kudu.
Bacewar Dak, ta zo ne bayan da sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, ya ba da sanarwa a ranar Talata na korar laftanal janar Johnson Kimani Ondieki dan asalin kasar Kenya, daga mukamin kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Sudan ta kudu.
Wani rahoton MDD ya ce, mista Ondieki, ya ki maida martani game da harin da sojojin gwamnati suka kaddamar a harabar bada agaji dake Juba babban birnin Sudan ta kudu, a lokacin wata arangama tsakanin dakarun gwamnati da na yan tawaye a watan Yuli. Kuma a lokacin harin ne aka yiwa wasu mata jami'an aikin bada agaji fyade.
Shi dai Dak, ya yi na'am da korar da aka yiwa Ondieki, matakin da ake zargin shi ne ya harzuka gwamnatin Kenyan.
Kasar Kenya, ta ayyana cewar sallamar da aka yi wa jami'in ya fusata ta, kuma hakan ya sa ta yanke shawarar janye dakarunta daga Sudan ta kudu. (Ahmad)