A yayin taron, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, mista Li Baodong, ya ce tun bayan da aka cimma yarjejeniyar daidaita batun nukiliyar kasar Iran a shekarar da ta gabata, zuwa yanzu ana aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata. A cewarsa, kamata ya yi, kasashen 6 da bangaren Iran su kara yin mu'amala, don ganin an daidaita matsalolin da ake fuskanta a kokarin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.
Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan yarjejeniyar, kuma tana kokarin kare ta. Saboda haka, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da musayar ra'ayi tare da bangarori masu ruwa da tsaki, tare da kokarin shiga aikin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan batun nukiliyar kasar ta Iran.(Bello Wang)