A yau ne, Donald Trump, shugaban kasar Amurka mai jiran gado ya gabatar da manufofin da zai kaddamar a cikin kwanaki 100 bayan da ya hau kujerar mulkin kasar, ciki had da sanarwar neman ficewa daga yarjejeniyar cinikayya ta TPP.
A cikin wani hoton bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, mista Trump ya ce, za mu fito da yarjejeniyar ciniki mai adalci, a kokarin dawo da guraben aikin yi da kuma raya masana'antu a kasar ta Amurka.
A ranar 9 ga watan Nuwamban wannan shekarar ce Mista Trump ya lashe zaben shugabancin Amurka, yanzu haka yana shirin nada ministocin gwamnatinsa. Kuma a ranar 20 ga watan Janairun shekara mai zuwa ne zai yi rantsuwar kama aiki. (Tasallah Yuan)