in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin da Trump sun zanta ta wayar tarho game da karfafa dangantar Amurka da Rasha
2016-11-15 11:36:00 cri
A jiya Litinin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump, sun tattauna ta wayar tarho, inda bangarorin biyu suka amincewa juna game da yin hadin gwiwa da yadda zasu karfafa dangantaka tsakanin kasashensu biyu.

Shugabannin biyu, sun tabo batun yadda zasu farfado da dangantakar dake tsakanin kasashen nasu, musamman wajen kulla kyakkyawar dangantakar kasuwanci da bunkasuwar tattalin arziki, wanda hakan zai taimakawa al'ummomin manyan kasashen biyu su ci gajiyar mu'amala dake tsakanin bangarorin biyu.

Putin da Trump, sun kuma tabo batun yadda zasu hada gwiwa wajen yakar abokan gabarsu, wadanda suka hadada ta'addanci, da tsattsauran ra'ayi, sannan sun zanta game da batun halin da ake ciki a rikicin Syria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China