in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kuskuren dan-Adam ne ya haddasa hadarin jiragen kasa na Jamus
2016-02-10 11:46:08 cri
Rahotanni daga kasar Jamus na cewa, kuskuren dan-Adam ne ya haddasa hadarin jiragen kasa da ya faru jiya Talata a jihar Bavaria da ke kudancin kasar wanda ya yi sanadiyar rasuwar rayukan mutane a kalla 10.

Kafofin watsa labaran kasar sun bayyana cewa, wani ma'aikacin layin dogo ne ya dakatar da na'urar kaucewa aukuwar hadari domin ba da dama ga wani jirgin ya wuce.

Ko da yake, bayanai na nuna cewa, jirgin bai wuce layin da jiragen ke kai a kan lokaci ba kafin su koma tagwayen layin dogo.

Kakakin 'yan sandan jihar Bavaria ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba a ji duriyar mutum guda ba. Yayin mutane 17 kuma suka ji mummuna rauni.

Kimanin mutane 150 ne suke cikin jiragen kasan guda biyu lokacin da suka yi taho mu gama da misalin karfe 6 da mintuna 40 na safe agogon wurin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China