in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu jiragen kasa sun yi taho mu gama a kasar Jamus
2016-02-09 17:54:34 cri
Rahotanni daga kasar Jamus na cewa, mutane 4 sun mutu kana a kalla 100 suka jikkata, bayan da wasu jiragen kasa guda biyu a birnin Rosenheim da ke kudancin kasar suka yi taho-mu gama.

Hadarin wanda ya faru da sanyin safiyar yau Talata ya kuma haddasa tagarai da dama kaucewa daga layin dogon.

An ruwaito kakakin hukumar jiragen kasa ta kasar Jamus yana bayyana cewa, ba a san abin da ya haddasa jiragen kasan yin karo a kan layi guda ba.

Yanzu haka, ma'aitakan agaji na kan hanyarsu ta zuwa wurin da hadarin ya faru, kana an bukaci a tura jirage masu saukar ungulu don zakulo wadanda hadarin ya rutsa da su. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China