in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi jawabi a yayin kwarya-kwaryar taron kolin APEC
2016-11-21 10:18:59 cri

Jiya Lahadi, an bude kwarya-kwaryar taron koli karo na 24 na kungiyar APEC a Lima, babban birnin kasar Peru, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, tare kuma da ba da muhimmin jawabi mai taken "Neman makoma mai kyau, ciyar da cigaban yankin Asiya da Pasific", inda ya jaddada cewa, ya kamata a zurfafa dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen Asiya da Pasific, kana da neman samun moriyar juna ta hanyar bude kofa ga ketare, da inganta wadatuwar yankin ta hanyar hadin kai, da kuma kokarin neman ci gaba, ta yadda za a kafa makoma mai kyau domin bunkasuwar yankin.

Taken kwarya-kwaryar taron din shi ne "Neman bunkasuwa mai inganci da ci gaban dan Adam". Shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC da suka halarci taron sun yi musayar ra'ayoyi sosai kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi kalubalolin da ake fuskanta wajen gudanar da cinikayya cikin 'yanci da zuba jari a yanayin da ake ciki, da samar da isassun abinci, tinkarar sauyin yanayi da samu albarkatun ruwa, da kuma tabbatar da yin cudanya mai inganci tsakanin kasashen yankin da dai sauransu.

Baki daya shugabannin sun yi imanin cewa, yankin Asiya da Pasific na taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar ci gaban tattalin arzikin duniya. A wannan yanayin da ake ciki a yanzu, kamata ya yi a kafa tsarin tattalin arziki mai bude kofa na Asiya da Pasific, da adawa da ra'yin ba da kariya fiye da kima ga cinikayya, da zurfafa yunkurin gudanar da cinikayya cikin 'yanci a yankin, da kuma inganta yin cudanya a dukkan fannoni, da nufin zuba sabon karfi kan bunkasuwar tattalin arzikin Asiya da Pasific da kuma na duniya baki daya.

Baya ga haka kuma, a yayin taron din aka kaddamar da sanarwar kwarya-kwaryar taron koli karo na 24 na APEC. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China