A lokacin ganawar Firaminista Li ya bayyana cewa, Sin na fatan sa kaimi ga yin kwaskwarima kan manyan ayyukan more rayuwar jama'a kamarsu sufuri da tasoshin samar da wutar lantarki ta hanyar kafa cibiyar jirgin sama a shiyya-shiyya, da cibiyar sha'anin kere-kere da sauransu, domin kafa wani abin koyi a fannin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.
A nasa bangare shi kuma, shugaba Mulatu ya bayyana cewa, Sin tana kan gaban kome da Habasha za ta dauka wajen yin hadin gwiwa tsakaninsu. Ana bunkasa dangantaka tsakaninsu ta hanyar amincewa da samun moriyar juna.
Don haka inji shi Habasha na fatan sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin ta da Sin tare da ma sauran kasashen Afirka da ita kanta kungiyar tarayyar kasashen Afirka.(Fatima)