in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta koka game da wagegen gibin dake tsakanin yara 'yan makaranta a Sudan ta Kudu
2016-10-12 10:38:53 cri

Asusun kula da harkokin kananan yara na MDD wato UNICEF, ya bayyana rashin daidaito tsakanin jinsi, auren wuri, da kuma ayyukan gida da ake sa yara mata a matsayin dalilan dake haifar da wagegen gibi wajen hana yara mata shiga makarantu a kasar Sudan ta Kudu.

Da yake jawabi a lokacin bikin tunawa da ranar yara mata ta kasa da kasa a Juba, Vinoba Gautam, manajan shirin ba da ilmi na asusun UNICEF a Sudan ta Kudu ya ce, kashi 35 cikin 100 na yara mata ne kadai suke samun damar shiga makarantu a Sudan ta Kudu, sannan malamai mata ba su wuce kashi 15 cikin 100 na adadin malaman makarantu kusan dubu 40 da ake da su a duk fadin kasar ba.

Gautam ya kara da cewa, tashe-tashen hankula, da munanan al'adu, da kuma yi wa yara mata auren wuri na daga cikin dalilan da suka haifar da rashin daidaito a tsakanin jinsi cikin yaran kasar, sai dai ya bukaci hukumomi da iyayen yara, da su guji yi wa 'yayansu mata auren wuri, kuma su ba da yara mata damar shiga makarantu domin cike gibin dake tsakaninsu da 'ya'ya maza domin kubutar da su daga kangin talauci.

A cewarsa, malaman makarantu mata, abin koyi ne ga yara mata dake makarantu. Ya zama tilas gwamnati da kungiyoyin ba da tallafi su kara azama domin samar da karin malamai mata, da shugabannin makarantu mata, da kuma jami'ai mata masu kula da sashen ilmi.

In ji Gautam, kusan rabin makarantu dake Sudan ta Kudu ba su da muhalli mai tsabta wanda hakan na hana yara mata su samu damar ci gaba da karatuttukansu.

Ya kara da cewa, asusun na UNICEF da sauran kungiyoyin ba da agaji suna ci gaba da kokari wajen samar da yanayi mai kyau a makarantu domin ya ja hankalin dalibai mata don su samu damar kammala karatuttukansu. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China