in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 73 sun rasu sakamakon fashewar motar dakon mai a Mozambique
2016-11-18 12:54:20 cri
Jiya Alhamis, gwamnatin kasar Mozambique ta fidda wata sanarwa dake cewa, wata motar dakon mai ta kama wuta a lardin Tete dake yamma maso kudancin kasar, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 73, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Rahotanni na cewa, motar ta kife ne a lokacin da take kan hanyarta daga birnin Beira dake tsakiyar kasar Mozambique zuwa kasar Malawi, kuma isar wasu mazauna wurin ke da wuya domin dibar man, sai ta kama da wuta, lamarin da ya haddasa rasuwa da jikkatar mutane masu yawa.

Haka kuma, bayan aukuwar hadarin, gwamantin kasar Mozambique ta sanar da cewa, an riga an kai wadanda suka jikkata asibiti. A halin yanzu kuma, gwamnatin kasar ta tura ma'aikata wurin da hadarin ya auku domin gudanar da bincike. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China