in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Mozambique kimanin miliyan 2.5 ne suke bukatar taimako El Nio, in ji jami'in MDD
2016-10-28 11:03:24 cri
Manzon musamman mai kula da matsalar El Nio da sauyin yanayi na MDD Machria Kamau ya bayyana cewa, ba a samu amfanin gona kamar yadda ake fata ba a kasar Mozambique, sakamakon matsalar fari a sanadin yanayin El Nio da ta shafi kasar, wannan ya sa kimanin mutane miliyan 2.5 a kasar ta Mozambique suke bukatar taimako matuka a halin yanzu.

Haka kuma, bayan ganawarsa da shugaban kasar Mozambique Felipe Jacinto Newsy a babban birnin kasar, Maputo a ran 26 ga wata, Mr. Kamau ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su kara samar da taimakon jin kai ga wadanda suke fama da matsalar a kasar.

Bugu da kari, ya ce, a farkon shekarar bana, gamayyar kasa da kasa sun yi alkawarin samar wa kasashen Afirka dake fama da matsalar El Nio taimakon abinci, amma ya zuwa yanzu, kimanin kashi 50 bisa dari na alkawarin da aka yi ne kawai aka bayar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China