in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jinjinawa Mozambique da Burundi bisa goyon bayan Sin kan batun tekun kudu
2016-05-19 20:49:06 cri
A yau Alhamis 19 ga watan nan ne kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin Hong Lei, ya jinjina wa gwamnatocin Mozambique da Burundi bisa goyon bayan su ga matsayin da Sin ke dauka kan batun tekun kudu na kasar, tare da kiyaye adalci a duniya. Mr. Hong ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka shirya.

A jiya Laraba ne dai shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na Mozambique, Filipe Jacinto Nyusi, inda suka yi musayar ra'ayi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da harkokin shiyya shiyya da na duniya da suka fi jawo hankulansu.

Cikin kalaman sa shugaban na Mozambique ya bayyana cewa, kasar sa na nuna goyon baya ga ra'ayin Sin na daidaita batun yankuna mallakar kasar, da batun yankin teku ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, bisa kuma yarjejeniyar da bangarorin da batun ya shafa suka daddale, da matsayar da suka cimma.

A kwanan baya kuma, gwamnatin Burundi ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su daidaita batutuwan ta hanyar shawarwari cikin lumana, bisa sanarwar ayyukan bangarori daban daban dake daf da tekun kudun. Ta kuma jaddada cewa kamata ya yi kasa da kasa su girmama kasashe masu ikon kansu game da 'yancinsu na zaben hanyar daidaita gardama. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China