Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, yanzu haka, kasashen Afirka na kokarin gano hanyar da ta dace su bi domin samun ci gabansu, wadanda kuma suke hada kan juna tare da gaggauta dunkulewar nahiyar, abin da ke sa kasar ta Sin farin ciki, kuma kasar na nuna imani ga makomar bunkasuwar kasashen Afirka. Ya ce kasar Sin a nata bangaren za ta yi kokarin tabbatar da nasarorin da aka cimma a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Johannesburg, domin samun moriyar hadin gwiwa da juna.
A nasa tsokaci Mr. Filipe Nyusi godiya ya yi ga Sin, kan tallafin da ta ba wa kasarsa ta fuskar neman 'yancin kan al'umma, da kuma ci gaban kasar, kuma ya ce, shawarar da shugaba Xi ya gabatar game da hadin gwiwar Sin da Afirka a gun taron kolin Johannesburg, ta sanya kuzari ga ci gaban kasashen Afirka, da kuma hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Afirka da ma kasar Sin. Kaza lika Mozambique na fatan inganta hadin gwiwa da Sin ta fannonin ciniki da masana'antu, da aikin gona da kamun kifi, da sarrafa abinci da makamashi, da kimiyya da manyan ababen more rayuwa da sauransu. (Lubabatu)