in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan damben kasar Sin Zou Shiming ya lashe kambin dambe ajin marasa nauyi na duniya
2016-11-16 15:57:37 cri
Dan wasan damben kasar Sin ajin marasa nauyi, wanda a baya ya taba lashe lambar zinari har karo 2 a gasannin Olympic Zou Shiming, ya samu nasarar doke takwaransa na kasar Thailand Prasitsak Phaprom, a gasar cin kambin duniya da suka kara a daren ranar Litinin.

Da yake bayyana farin cikin sa game da wannan nasara da ya samu, Zou dan shekaru 35 da haihuwa, ya ce "Mafarki na ya zama gaskiya, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. Ban samu wani matsi ba. Na samu nutsuwa sosai a dukkanin zagayen danben da muka gudanar. Na samu nasarar lashe lambar zinari ta Olympic, yanzu kuma na samu kambin duniya".

A baya Zou ya gaza cimma nasarar samun wannan kambi. Lokacin da abokin damben sa Amnat Ruenroeng ya doke shi a watan Maris na shekarar 2015.

A baya ma dai Zou da Phaprom sun dambata sau dama, inda shekaru 2 da suka gabata a yankin Macau Zou ya doke Phaprom. Bayan wannan wasa kuma, Phaprom ya samu sanara a wasanni 12 da ya yi. Yayin da a daya hannun Zou shi ma ya sake samun nasara a wasan su na wannan karo da maki mafi rinjaye, kamar dai yadda alkalan damben suka tabbatar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China