Mr. Leung wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, bayan da babban kwamitin zartaswa na JKS ya zartas da wannan doka da safiyar yau din, ya kara da cewa ba za a lamunci duk wani yunkuri na karya dokar, ko cin zarafin kasar Sin ba, kuma duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci fushin hukuma.
Fashin bakin wannan doka dai ya tanaji martaba dokokin yankin Hong Kong na musamman na kasar Sin, tare da amincewa da dokokin yankin na Hong Kong na kasar Sin. Bayan haka kuma, tanajin dokar ya hada da rantsuwar martaba ka'idojin dokar, ciki hadda na tsayawa takarar zabuka wanda dokar ta fayyace.
Rahotanni dai sun bayyana cewa zababbun 'yan majalissar dokokin yankin na Hong Kong ta 6 su biyu, sun furta kalaman rashin martabawa ga kasar Sin da gangan, lokacin da suke rantsuwar kama aiki a ranar 12 ga watan Oktobar da ta gabata. Sai dai jami'in lura da rantsuwar kama aikin na su, bai amince da rantsuwar da suka yi ba. (Saminu Hassan)