Hong Lei ya tabbatar da hakan ne a yayin da yake mayar da martani game da tarzomar da ta barke a yankin Mong Kok na Hong Kong tun a ranar Talatar da ta gabata.
Hong ya kara da cewa, wasu kungiyoyin 'yan ta da zaune tsaye ne masu neman ta ware suka kitsa ta da tarzomar a Mong Kok dake yankin Hong Kong tun a ranar 9 ga watan nan na Fabrairu.
Sanarwar ta kara da cewar, masu zanga zangar sun yi wa tituna a yankin kawanya inda suka cinna wuta, tare da lalata motocin jami'an 'yan sanda bayan sun jefi su da duwatsu, lamarin da ya haddasa jikkata jami'an 'yan sanda kimanin 89 da wasu 'yan jaridu.
Mista Hong ya kara da cewa, al'ummar yankin Hong Kong mutane ne masu kaunar zaman lafiya. Don haka gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta goyi bayan matakin da hukumar gudanarwar yankin da jami'an 'yan sandan suka dauka wajen tabbatar da tsaro a yankin, domin bada tsaro ga lafiya da dukiyoyin al'ummar mazauna yankin Hong Kong, sannan ta bukaci a zartar da hukunci kan duk wasu bata gari da aka samu da hannu wajen karya doka domin samun dawwaumammen zaman lafiya a Hong Kong. (Ahmad Fagam)