in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta musanta rahoton Birtaniya game da yankin Hong Kong
2016-02-13 12:27:52 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya musanta kalaman dake kunshe cikin wani rahoton watanni shida-shida, da gwamnatin Birtaniya ta gabatar ga majalissar dokokinta game da yankin Hong Kong na kasar Sin.

Da yake mai da martani kan rahoton a jiya Jumma'a, Mr Hong ya yi kira ga Birtaniya da ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin da suka shafi yankin Hong Kong. Ya ce Sin na matukar adawa da wannan rahoto mai cike da kalamai marasa tushe ko makama.

Bugu da kari Mr. Hong ya ce yankin Hong Kong, yankin musamman ne na kasar Sin, kuma duk wani batu da ya shafi yankin, batu ne na cikin gidan kasar Sin, wanda babu wata kasar waje da ke da ikon tsoma baki cikinsa.

Daga nan sai ya jaddada kira ga mahukuntan Birtaniya, da su kaucewa furta kalamai ko daukar matakan kutse cikin harkokin da suka shafi Hong Kong.

Mr. Hong ya kara da cewa tun dawowar Hong Kong karkashin ikon mulkin Sin a watan Yulin shekarar 1997, tsarin "kasa daya tsarin mulki biyu" da ake bi, ya haifar da manyan nasarori kamar yadda duniya ta shaida hakan. Kaza lika yankin na ci gaba da samun bunkasa, yayin da al'ummunsa ke amfana daga dukkanin kariya ta hakkokin bil Adama, da yancinsu na samun kyakkyawar rayuwa kamar yadda doka ta tanada. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China