in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin na cike da imani wajen warware bore a Hong Kong, in ji gwamnan yankin
2014-10-20 11:02:26 cri

A daren ranar 18 da kuma asubar ranar 19 ga wata, hukumar 'yan sandan Hong Kong, yankin musamman na kasar Sin ta kama wasu 'yan bore maza 4 a unguwar Wangjiao dake tsakiyar yankin, yayin kuma wannan hargitsin, 'yan sanda guda 5 ne suka ji rauni.

Babban jami'in 'yan sandan ofishin kula da dangantakar jama'a na hukumar kula da harkar tsaro ta gwamnatin yankin musamman na Hong Kong Xu Zhende ya bayyana a ranar 19 ga wata cewa, kawo yanzu unguwar da ake yin bore ta Wangjiao tana cikin hadari, 'yan bore na shirin gudanar da hargitsi a ko da yaushe.

A ran nan kuma, gwamnan yankin Hong Kong Leung Chun-ying shi ma ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana sa ido a halin da Hong Kong ke ciki sosai, kuma tana cike da imani cewa, ita da gwamnatin yankin za su daidaita boren yadda ya kamata, ban da haka, gwamnan ya kara da cewa, har kullum wasu kasashen waje na tsoma baki a cikin harkokin siyasar Hong Kong, yanzu ma haka akwai hannunsu.

A ranar 18 ga wata, mamba a majalisar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi ya yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, inda ya yi masa bayani kan matsayin da gwamnatin kasar Sin ke dauka kan batun Hong Kong.

Yang Jiechi ya jaddada cewa, muna nuna kiyayya ga dukkan ayyukan saba wa doka da suka faru a Hong Kong, kuma muna goyon bayan gwamnatin yankin da ta daidaita rikicin bisa doka, tare kuma da kiyaye zaman karko a yankin. Harkar Hong Kong harkar gida ce ta kasar Sin, bai kamata ba kasashen waje su tsoma baki a ciki. Yang Jiechi yana fatan Amurka za ta taimaka wajen kiyaye tsaro da wadata a Hong Kong, ta kaucewa nuna goyon baya kan ayyukan saba wa doka a yankin. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China