in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci Birtaniya da ta daina tsoma baki cikin harkokin Hong Kong
2016-10-13 20:13:43 cri

Kwanan baya, gwamnatin kasar Birtaniya ta kaddamar da rahotonta kan yankin musamman na Hong Kong na rabin shekara.

Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Alhamis 13 ga wata a nan Beijing cewa, harkokin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, wadanda babu wanda yake da ikon tsoma baki cikinsu. Don haka kasar Sin ta bukaci Birtaniya da ta yi taka tsan-tsan, ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin Hong Kong.

Geng Shuang ya kara da cewa, bayan da Hong Kong ta koma karkashin mulkin kasar Sin, an samu nasarori sosai wajen aiwatar da manufar "Kasa daya, tsarin mulki biyu". Kasar Sin ba za ta canza aniyarta, da kuma karfin zuciyarta wajen ci gaba da aiwatar da manufarta ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China