in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AFDB: Tattalin arzikin kasashen Afirka zai samu farfadowa a shekarar 2017
2016-11-02 10:58:55 cri
Jaridar The Guardian ta kasar Tanzania, ta bayar da labari a kwanan baya cewa, rahoton hasashe game da tattalin arziki na shekarar 2016 wanda bankin AFDB ya fitar, ya nuna cewa akwai tunanin tattalin arzikin kasashen Afirka zai ragu zuwa matsayi mafi kankanta a bana, kana kuma ya samu farfadowa a shekara mai zuwa, inda zai zamo biye da na kudu maso gabashin Asiya, ta yadda nahiyar Afirka za ta kasance yanki na biyu wajen samun saurin karuwar tattalin arziki.

Rahoton ya ce, a shekarar 2016, karuwar jamillar kudin kayayyakin da ake samarwa a gida ( GDP) a nahiyar Afirka ya ragu daga kaso 3.6 cikin dari a bara, zuwa kaso 1.9 cikin dari a bana, amma mizanin na GDP zai karu zuwa kaso 3.2 cikin dari a shekara mai zuwa. An yi wannan hasashe ne bisa la'akari da farfadowar tattalin arzikin duniya, da karuwar farashin manyan kayayyakin cinikayya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China