in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fuskantar karancin hatsi in ji wani jami'in kasar
2016-02-29 10:20:34 cri
Darakta a ofishin gudanar da ayyuka na ma'aikatar gona ta kasar Sin Chen Xiwen, ya bayyana cewa kasar Sin na fuskantar karancin hatsi, duk kuwa da yawan yabanyar da aka samu a kakar bana, inda bisa kididdiga hatsin da aka samu ya yi kasa da wanda aka yi amfani da shi a bara, da kusan tan miliyan 20 zuwa miliyan 25.

Mr. Chen, wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi yayin wani taron karawa juna sani game da fannin noma, ya kuma ce jimillar hatsin da kasar ta samu a bara ya karu da kaso 2.4 bisa dari, inda adadin sa ya kai tan miliyan 621, wanda ya nuna ci gaban da kasar ke samu cikin shekaru 12 a jere. Sai dai duka da hakan a cewar sa akwai bukatar shigo da karin hatsin daga ketare.

Jami'in ya kara da cewa a bara, adadin hatsin da aka shigo da shi kasar ta Sin ya kai tan miliyan 120, inda waken soya ke kan gaba da kaso 70 cikin dari na hatsin da aka sayo daga ketare.

A bara ne dai masu tsara dokokin kasar ta Sin suka jaddada aniyar su ta tabbatar da samar da isasshen abinci yayin wani taron raya karkara. Cikin kuma matakan da mahukuntan kasar ke dauka domin cimma wannan buri a cewar Mr. Chen, akwai bada kariya ga gonakin noma, da tabbatar da samun isasshiyar yabanya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China