A yayin taron, an gabatar da rahoto dangane da harkokin hadin gwiwar masana'antu a tsakanin lardin Zhejiang na kasar Sin da kasashen Afirka a shekarar 2016, rahoton ya samar da shawarwari masu inganci ta fannin inganta harkokin cinikayya a tsakanin lardin Zhejiang da kasashen Afirka, tare kuma da saukakawa masu masana'antu na sassan biyu yadda za su zuba jari da gudanar da harkokin kasuwanci a kasashen juna, haka kuma ya samar da shawarwari ga sauran larduna da birane na kasar Sin kan yadda za a aiwatar da hadin gwiwar masana'antu da kasashen Afirka.(Lubabatu)