in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya: Mutane miliyan 1.3 suke cikin bukatar agajin abinci cikin gaggawa
2016-10-17 11:25:34 cri
Gwamnatin Kenya ta sanar da cewa kimanin mutane miliyan 1.3, a yawancin yankuna dake fama da karancin ruwa, suke bukatar wani agajin abinci cikin gaggawa sakamakon dakarewar fari a cikin yawancin yankunan kasar. Gwamnatin Kenya ta shirya ayyuka daban daban domin tabbatar da ganin ba wanda ya mutu cikin kasar bisa dalilin fari, in ji Mwangi Kiunjuri, wani jami'in ma'aikatar batun rabo da fasali, a yayin wani taron manema labarai a wannan mako a birnin Nairobi.

Amma duk da haka ya bayyana cewa matsalar tsaron abinci ta kyautatu, inda ya kara da cewa yawan mutanen da suka yi fama da fari ya ragu, daga miliyan 2.5 a shekarar bara zuwa miliyan 1.3 a wannan shekara.

Jihohi takwas ne suka fi fama da matsalar fari, inda mazauna wuraren suke tsananin bukatar taimakon abinci na gaggawa da kuma kudade.

Mista Kiunjuri ya sanar da cewa, domin rage kaifin mugun sakamakon fari, baitulmalin kasa ya kebe dalar Amurka miliyan 2.5 a cikin watan Augusta domin saye da rabon abinci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China