161028-JKS-za-ta-kara-kyautata-kaidarta.m4a
|
Jiya Alhamis ne aka rufe cikakken zaman taro na 6 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS na 18 a nan birnin Beijing, inda a karo na farko shugabannin JKS suka tattauna kan yadda za a sake gina jam'iyyar domin kara kyautata ka'ida da kuma tsarinta.
Bayan taron, an kuma zartas da muhimman takardu biyu wadanda za su ba da jagoranci kan yadda za a tafiyar da harkokin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, takarda ta farko ita ce, "wasu ka'idoji game da harkokin siyasa a cikin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a sabon halin da ake ciki yanzu", ta biyu kuma ita ce, "wasu ka'idoji game da sa ido kan halin da 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suke ciki". Kana an fitar da tsarin gudanar da harkokin JKS a hukumance wato za a kafa kwamitin tsakiyar JKS a karkashin jagorancin babban sakataren JKS Xi Jinping, kuma an yi kira ga daukacin 'yan jam'iyyar da su hada kai domin kara kyautata ka'idojin jam'iyyar, tare kuma da kara kokari matuka tare da dukkanin al'ummar kasar ta Sin, ta yadda za a cimma burin bude sabon babi yayin da ake gina sha'anin gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin.
Tun bayan da aka kira babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, babban sakataren jam'iyyar Xi Jinping ya sha jaddada cewa, idan har ana son kara kyautata ka'idojin jam'iyyar, yana da muhimmanci matuka a gudanar da harkokin siyasa na jam'iyyar bisa ka'idojin da aka tsara, yanzu dai an zartas da "wasu ka'idoji game da harkokin siyasa a cikin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin bisa la'akari da sabon halin da ake ciki yanzu", hakan ya nuna cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta sake bullo da sabbin ka'idoji game da harkokin siyasa a cikinta bayan shekaru 36 da suka gabata.
Mataimakin darektan cibiyar nazari kan aikin gwamnati ta jami'ar Beijing Zhuang Deshui ya bayyana cewa, "Daga cikin batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa da aka tarar da su bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, an gano cewa, dalilin da ya sa wasu manyan shugabannin jam'iyyar suka aikata laifuffuka, shi ne domin ba su gudanar da harkokin siyasarsu yadda ya kamata ba. Idan har suka gudanar da harkokin siyasarsu a cikin jami'iyyar bisa ka'ida, ko kuma aka shawo kansu kafin su aikata laifuffuka, to, kila ba za a kai su gaban kotu ba. A saboda haka kamata ya yi mu kara mai da hankali kan ka'idojin jam'iyyarmu, ta haka ne za a kago wani muhallin siyasa na gari a kasar ta Sin."
Yayin taron, an kuma jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, idan ana son kara kyautata harkokin siyasar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, abu mafi muhimmanci shi ne a kara sa ido kan manyan shugabannin jam'iyyar, musamman ma mambobin kwamitin tsakiyar JKS, da hukumar siyasar kwamitin tsakiyar JKS, da kuma zaunannen kwamitin hukumar siyasar kwamitin tsakiyar JKS. A baya, sabbin shugabannin kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun tsara ka'idoji guda takwas tun bayan da suka fara gudanar da mulki a kasar ta Sin domin samar da muhallin siyasa na gari a kasar.
Shehun malamin dake aiki a kwalejin nazarin tafiyar da harkokin kasa ta kasar Sin Zhu Lijia yana ganin cewa, kamata ya yi shugabannin kwamitin tsakiyar JKS su kyautata aikinsu kuma su kasance abin misali ga al'ummar kasarsu, wannan lamarin yana da muhimmanci matuka. Zhu Lijia yana mai cewa, "Shugabanni, musamman ma mambobin kwamitin tsakiyar JKS, suna taka muhimmiyar rawa yayin da ake kokarin raya tattalin arziki da zaman takewar al'ummar kasar Sin, haka kuma suna zama abin misali ga sauran al'ummar kasar, shi ya sa wajibi ne su kara kyautata halayensu, saboda za su yi tasiri ga sauran jama'a."
Kazalika, a yayin taron, an tsai da cewa, za a kira babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 a shekarar 2017 mai zuwa, kuma an yi kira ga daukacin 'yan jam'iyyar da su hada kai karkashin jagorancin babban sakataren JKS Xi Jinping domin fito da wani muhallin siyasa na gari, tare kuma da gina sha'anin gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin yadda ya kamata.
Shehun malamin jami'ar horas da shugabnanin 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xin Ming ya bayyana cewa, "Wannan taron da aka gudanar yana da babbar ma'ana, saboda a yayin wannan taron ne aka ba da umurnin kara kyautata ka'idojin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ana iya cewa, taron ya samar da tabbaci gare mu a fannonin tunani da tsari yayin da muke kara hada kai karkashin jagorancin Xi Jinping, sannan ya alamanta cewa, an bude wani sabon babi na gina babban sha'ani a kasar Sin a karkashin jagorancin JKS." (Jamila)