Madam Hua ta bayyana haka ne a yau Talata a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa, ta ce, an shirya taron kolin a daidai lokacin da ake neman hanyoyin raya tattalin arzikin duniya, da canja tsarin G20, saboda haka taron ya jawo hankulan al'ummomin kasashen duniya sosai.
A yayin taron, kasar Sin ta sanya bangarori daban daban da suka halarci taron wajen tattauna manufofin samun ci gaban tattalin arzikin duniya da hadin kai a tsakaninsu, kana an cimma muhimmin ra'ayi bai daya kan wasu batutuwa. (Bilkisu)