in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa 'yan wasan Brazil biyu ba za su buga mata wasan neman gurbi a wata mai zuwa ba
2016-09-28 19:49:12 cri

Ga alama 'yan wasan Brazil su biyu wadanda kuma ke taka leda a kulaf din Real Madrid, wato Casemiro da Marcelo, ba za su halarci wasanni biyu da Brazil din za ta buga da Bolivia da kuma Venezuela cikin watan Oktoba mai zuwa ba, wasannin da za a buga su domin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2018 a kasar Rasha.

Real Madrid dai ta bayyana cewa Casemiro ya samu rauni a wasan da ta buga da Esoanyol, wanda kuma Madrid din ta samu nasara da ci 2-0, a gasar La Liga ta kasar Sifaniya da suka buga a ranar Lahadi. An ce mai yiwuwa dan wasan ya yi jiyya ta kusan wata guda.

Shi ma Marcelo ya ji ciwo ne a kokon gwiwar sa, yayin wasan da Madarid din ta tashi kunnen doki 1-1 ita da Villarreal a ranar Laraba. Dama dai Brazil ta rasa dan wasan Bayern Munich Douglas Costa, wanda shi ma dai ke da rauni a yanzu haka.

Brazil wadda ta dauki kofin duniya har karo 5, za ta kara da Bolivia a gida a ranar 6 ga watan Oktoba, kafin kuma wasan ta da Venezuela kwanaki 5 bayan wannan rana. Ya zuwa yanzu dai Brazil din na matsayi na biyu a teburin rukunin ta, da maki 15 cikin wasanni 8 da ta buga, inda take biye da Uruguay.

Bisa tsarin wasannin na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a buga a shekarar 2018 a kasar Rasha, kungiyoyi 4 dake kan gaba a rukunin su ne za su wakilci rukunin su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China