in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya liyafar murnar cika shekaru 45 da MDD ta maido wa Sin halatattun hakkokinta a duniya
2016-10-26 13:20:24 cri

A daren jiya Talata ne, aka shirya liyafa a birnin Beijing don murnar cika shekaru 45 da MDD ta maido wa Sin halatattun hakkokinta a duniya. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi wanda ya shugabanci liyafar, ya nuna cewa, shekaru 45 da suka gabata, wato ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 1971, rana ce ta musamman a tarihin diplomasiyyar kasar Sin. An tsai da kudurin maido wa Sin halatattun hakkokinta a duniya ne a yayin babban taron MDD, wanda ya bude wani sabon babi a tarihin MDD, kuma daga wancan lokaci ne kasar Sin ta kara hadin gwiwarta da MDD.

A cikin jawabin da ya bayar, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, a cikin wadannan shekaru 45 da suka gabata, ko da yaushe kasar Sin tana himmantuwa wajen shimfida zaman lafiya a duniya, da ba da gudummawa ga ci gaban duniya, da kiyaye dokokin duniya, da kuma mara baya ga harkokin da suka shafi MDD. Ya kara da cewa,

"Kasar Sin tana nacewa ga warware duk sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kuma tana amfani da hakika da basira wajen warware batun nukiliyar Iran da rikicin kasashen Syria da na Sudan ta Kudu da dai sauransu. Haka kuma Sin ta gudanar da taron kolin G20 cikin nasara, inda ta shigar da batun ci gaba a cikin tsarin manyan manufofin duniya, baya ga gabatar da matakan da kasar Sin ta yi amfani da su wajen aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030. Bugu da kari, kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen kiyaye tsari da dokokin kasashen duniya wadanda ke dora muhimmanci kan makasudin tsara kundin da ya kunshin dokoki da tsarin MDD, tare kuma da dokokin kasa da kasa. Haka zakila, kasar Sin kasa ce da ke kan gaba wajen aika yawan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya a cikin zaunannun mambobi biyar na kwamitin sulhu na MDD, kuma ita ce kasar da ke sahun gaba wajen cimma manufofin muradun karni na MDD wato MDGs da kuma kau da mutane mafi yawa daga kangin talauci a cikin dukkan mambobin MDD.

Yang Jiechi ya kuma jaddada cewa, yanzu aikin bunkasuwar kasar Sin da kuma sha'anin MDD na cikin wani muhimmin zamani, za a bude wani sabon babi a ci gaban dangantakar da ke tsakanin Sin da MDD, sa'an nan Sin za ta kara ba da gudummawa ga harkokin majalisar. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China