in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
BAD ya samarwa Morocco da kwararru a fannin yanayi domin shirya taron COP22
2016-10-24 10:56:18 cri

Bankin ci gaban Afrika (BAD) ya samarwa gwamnatin Morocco da kwararru a fannin yanayi, ta yadda za a taimakawa kasar a cikin shirye shiryenta na gudanar da taron bangarorin yarjejeniyar ba da jagoranci ta MDD kan sauyin yanayi (CCNUCC) karo na 22 da aka sani da COP22, da birnin Marrakech zai karbi bakunci daga ranar 7 zuwa 18 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Bisa babbar kwarewarsu ta rage kaifi gaban sauyin yanayi, da zuba kudi kan sauyin yanayi, da muhalli, da karfafa karfi, da musanyar fasahohin zamani da bunkasa ayyuka, wadannan kwararru za su taimakawa gungun aikin COP22 cikin tsawon lokaci, kana za su ba da shawara ga gwamnatin Morocco kan wasu batutuwan dake da nasaba da COP22, in ji wata sanarwar bankin BAD a ranar Jumma'a. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China