in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin bude cibiyar bankin EIBC reshen arewa da yammacin Afrika a Morocco
2015-05-29 10:54:37 cri

A ranar Alhamis ne aka yi bikin bude cibiyar bankin shige da ficen kasar Sin (Export-Import Bank of China, EIBC) reshen arewa da yammacin Afrika a birnin Rabat a karkashin jagorancin shugaban bankin Liu Liange, jakadan kasar Sin dake kasar Morocco Sun Shuzhong, da kuma ministan kasar Morocco a ma'aikatar tattalin arziki da kudi, Idriss El Azami El Idrissi.

Wannan ita ce dai cibiya ta farko dake wajen kasar Sin da aka kafa a kasar Morocco wadanda ta kasance wata ma'aikatar hada hadar kudi ta kasar Sin. Wannan kuma bayan cibiyar bankin EIBC reshen kudanci da gabashin Afrika dake birnin Johannesbourg na kasar Afrika ta Kudu, cibiyar Rabat ta kasance wata ma'aikatar EIBC ta biyu dake wajen kasar Sin.

Cibiyar bankin EIBC dake Rabat za ta samar da harkokin kudi ga kasar Morocco da wasu kasashen arewacin Afrika, yammacin Afrika da kuma tsakiyar Afrika. Tare da sabon dandalin harkar kudi, bankin EIBC na kasar Sin zai samar da kwarewarsa, da kuma alfanunsa domin karfafa dangantaka tare da abokan hulda na cikin gida da gwamnatocin kasashe masu karbar rance, da karfafa da fadada kasonsa a kasuwanni, da kara sanya ido kan harkokin kudi tsakanin kasa da kasa da kuma rigakafin yaki da haduran na ayyukansa a Afrika, da kuma kara taimakawa kamfanoni da hukumomin kudin kasashen Afrika ta hanyar kara bunkasa huldar dangantaka tsakanin kudu da kudu.

Jakadan kasar Sin dake Morocco, Sun Shuzhong, ya yi kira ga kasar Morocco da sauran kasashen Afrika da su yi amfani da wannan dandalin kudi da EIBC ya kafa domin bunkasa musanyar kasuwanci da kuma dangantakar tattalin arziki tare da kasar Sin. A nasa bangare, mista Idriss El Azami El Idrissi ya bayyana a yayin bikin cewa, wannan cibiyar kudi ta farko ta kasar Sin a kasar Morocco na nuna kyakkyawar dangantaka, da ma kuma gamsuwar kasar Sin game da rawar da kasar Morocco ke takawa wajen karfafa dangantaka tsakanin Sin da Afrika, tare da nuna fatan ganin wasu bankunan kasar Sin za su kafa cibiyoyinsu a kasar Morocco nan da dan lokaci mai zuwa, domin taimakawa ci gaban huldar tattalin arziki tsakanin Sin da Morocco da kuma tsakanin Sin da Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China