in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta yi niyyar kira jakadanta dake Abuja domin shawarwari
2015-03-11 10:28:05 cri

Kasar Morocco ta yi niyyar kira jakadanta da ke Abuja cikin gaggawa domin neman karin haske daga wajensa, a cewar wata sanarwar ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Sanarwar ta bayyana a ranar Talata da yamma cewa, sabanin abin da hukumomin Najeriya suka gaya wa jakadan kasar Morocco dake Abuja da kuma kafofin kasar, Morocco ta tabbatar bisa tushen gaskiya cewa, ba a yi wata tattaunawa ba ta wayar tarho tsakanin Sarki Mohammed VI da shugaban Najeriya.

Mai martaba sarki ya kawar da goyon gayyatar hukumomin Najeriya bisa dalilin cewa, ana so amfani da hakan ne kan wata manufa ta zabe da harkokin siyasa na cikin gida da matsayin wannan kasa na nuna adawa game da 'yancin fadin kasar Morocco, in ji wannan sanarwa.

Masarautar Morocco ta bayyana mamakinta da yin allawadai da irin wadannan tabi'un da ke sabawa tunani da halayya na shugabannin da ya kamata su ciyar da dangantaka mai kyau tsakanin kasashe, in ji ministan Morocco.

Daga karshe, sanarwar ta bayyana cewa, bisa wadannan abubuwa ne, kasar Morocco ta dauki niyyar kira jakadanta dake birnin Abuja cikin gaggawa domin samun karin haske. A nata bangare, fadar masarautar kasar Morocco ta yi allawadai da maganganun karya na hukumomin Najeriya dake bayyana cewa, an yi hira ta wayar tarho tsakanin sarkin Morocco da shugaban Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China