in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco na karbar bakuncin dandalin cigaban Afrika a  karon farko
2014-10-13 14:21:30 cri

Kwamitin tattalin arziki na MDD reshen Afrika (CEA) na shirya dandalinsa domin cigaban Afrika na ADF-IX tun daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Oktoba a birnin Marrakech, wanda ya kasance dandali na farko da aka taba shirya a wajen cibiyarsa dake birnin Addis-Abeba na kasar Habasha. CEA ya bayyana jin dadinsa domin ganin shirya dandalin a babban birnin Morocco, kasar da ake dauka a matsayin wata muhimmiyar cibiyar cigaban kasuwancin Afrika. Yanayin siyasa na daidai, kuma kasancewar inda kasar take yana da kyau, tsarin shari'a na gudanar da harkoki da gine-gine sun samu bunkasuwa yadda ya kamata, in ji wata sanarwar da CEA ya gabatar.

An shirya dandalin tare da hadin gwiwar kwamitin tarayyar Afrika, bankin cigaban Afrika, da kuma muhimman abokan hulda ne domin bullo da wani tsarin cigaban Afrika dake bayyana wata yarjejeniya da kai ga wasu tsare-tsaren musamman domin aiwatarwa. Domin duka da hasashen samun bunkasuwa mai kyau, nahiyar Afrika har yanzu na fama da karancin kudi a kowace shekara har dalar Amurka biliyan 31 a bangaren wutar lantarki kawai, a yayin da sauran kasashe masu hannu da shuni suka kasa kai ga cimma nauyin kasa da kasa da suka dauka.

Dandalin zai tattara wakilai fiye da 700 da suka hada da shugabannin gwamnatoci, masu fada a ji, shugannin kamfanoni, kwarraru na kasashen Afrika da na sauran kasashen duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China