A jiya Laraba kasar Morocco ta kaddamar da wata gidauniyar addini, wacce za ta yaki karuwar tsattsauran ra'ayin addini a Afrika, sannan ta tabbatar da ganin harkokin addinin ba su wuce gona da iri ba a nahiyar ta Afrika.
Sarkin Morocco Mohammed VI shi ne ya jagoranci kafa gidauniyar a lokacin taron malaman addinai daga kasashen Afrika 31.
Cibiyar za ta hada kan malamai addinin Islama, ta yadda za su samu damar gudanar da al'amurran addini da karantar da mabiya muhimmancin zaman lafiya, da yin biyayya ga koyarwar addanin musulunci a kasar Morocco, dama sauran kasashen Afrika.(Ahmad Fagam)